Matar Gaddafi na neman bayani game da gawarsa

Marigayi Mu'ammar Gaddafi
Image caption marigayi tsohon shugaban kasar Libya Mu'ammar Gaddafi

Matar marigayi tsohon shugaban kasar Libya Mu'ammar Gaddafi ta bukaci bayanin inda gawarsa take shekaru biyu bayan an hambarar da gwamnatinsa tare da kashe shi.

Safia Farkash wacce ta samu mafaka a wata kasa ta bukaci hakan ne a wata wasika da ta aika wa kafar yada labaran kasar Rasha mai suna The Voice of Russia.

An cafke kanar Gaddafi ne tare a wani hari da jami'an NATO suka kai inda aka hallaka shi kafin daga bisani aka binne gawar sa a wani kebantaccen wuri da ba a bayyana ba a kasar ta Libya.

Matar ta sa ta kuma bukaci tarayyar Afurka da ta binciki kisan da ta ce masu aikata muggan laifuffuka ne suka yi masa.