Mexico ta soki Amurka kan leken asirinta

Shugaba Enrique Pena Nieto
Image caption Shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto

Kasar Mexico ta yi kakkausar suka kan zargin leken asirinta da Amurka ke yi bayan da aka wallafa wasu zarge zarge da ke cewa hukumomin leken asirin Amurka sun yi ta satar bayanai ta addireshin Email na tsohon shugaban kasar Mexico.

Wata Mujallar kasar Jamus mai suna Der Spiegel ta rawaito cewa wasu muhimman takardu data samu daga tsohon jami'in leken asirin Amurka Edward Snowden, sun nuna cewa an yi ta satar bayanan tsohon shugaban kasar Mexico Felipe Calderon a lokacin da yake kan karagar mulki.

Ministan harkokin wajen kasar Mexico ya ce babu yadda za'a yi kasar sa ta amince da batun leken asirri a dangantakar dake tsakaninta da makwabatanta ko kuma wasu kawayenta.

Kasar ta kuma bukaci shugaba Obama da ya kammala binciken da ya yiwa takwararsa na kasar Mexican Enrique Pena Nieto alkawari yi fiye da wata guda.

An kafa hujjar farko kan leken asiri ne kan bayanan sirri da Edward Snowden ya bankado wadanda suka ce Amurka na satar bayanan Mr Pena Nieto, a lokacin da ya tsaya takarar neman mukamin shugaban kasa.

Haka kuma rahotanni sun yi nuni da cewa, hukumomin leken asirin Amurka sun yi ta satar bayanai ta adireshin Email na shugaban kasar Brazil.