Boko Haram: Najeriya za ta binciki sojoji

Mr Abba Moro
Image caption Ministan harkokin cikin gida a Najeriya Mr Abba Moro

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike kan zargin mutuwar daruruwan mutane a wuraren da ake tsare da wadanda ake zargi da aikata laifuffuka, yayin da sojoji ke fafutikar ganin sun kawadda masu tada kayar baya a arewacin kasar.

Ministan harkokin cikin gida Mr Abba Moro ya ce masu binciken za su hada da manyan jami'an hukumar gidan yari ta kasar.

Mr Moro ya furta hakan ne bayan wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta fitar, wanda ya yi zargin cewa mutane akalla 950 galibi wadanda ake zargi da alaka da kungiyar Boko Haram ne sun mutu a kurkutu a farkon watanni shida na wannan shekara.

Sai dai Ministan ya amince cewa lallai za'a iya samun wadanda suka mutu amma a cewarsa, basu kai daruruwa ba.

A rahoton nata, Amnesty International ta ce yawancin mutanen sun mutu ne saboda rashin isasshiyar iska ko abinci ko kuma kisan gilla a hannun jami'an tsaron.

Karin bayani