Tsaffi sun yi aure bayan shekaru 80

Image caption Ango da Amarya tare da jikokinsu

Wasu tsaffi 'yan kasar Paraguay, sun yi aure bayan shafe shekaru tamanin suna zama tare.

Zaune a kujerar guragu, Jose Manuel Riella mai shekaru 103, ya auri Martina Lopez, mai shekaru 99.

An daura aurenne a wajen shakatawa.

Bukin ya samu halatar 'ya'yan ma'auratan su takwas, da jikokinsu 50, tattaba kunne 35, da kuma 'ya'yan tattaba kunne 20.

Jami'in cocin da ya daura musu aure, ya ce sune amarya da ango mafi shekaru da ya sani.

Ma'auratan sun riga sun yi auren al'ada shekaru 49 da suka wuce, amma sai yanzu ne suka daura aure bisa tsarin addinni.