Akwai alamun samun maslaha a Amurka

Majalisar dokokin Amurka
Image caption Majalisar dokokin Amurka

'Yan majalisar dattawa na jam'iyyar Republican da na Democrat a Amurka sun cinma yarjejeniya domin kauce ma yanayin da Amurka zata gaza biyan bashin da ke bin ta, da kuma kawo karshen rufe wasu ma'aikatun gwamnati.

Jagoran masu rinjaye ,Harry Reid na jam'iyyar Democrat, ya ce cinma maslahar zai kawo daidaituwar da tattalin arzikin Amurka ke matukar bukata.

Kafin shirin yayi tasiri, tilas sai majalisar wakilai, wadda 'yan Republican ke da rinjaye, ta amince da shi.

Wani kakakin fadar White House, ya ce shugaba Obama, yayi marhabin da yarjejeniyar, yana mai kira ga majalisar dokokin da ta hanzarta amincewa da shi.