Masar na tsare 'yan gudun hijira - Amnesty

Wasu 'yan gudun hijirar Syria
Image caption Miliyoyin 'yan Syria ne ke gudun hijira a kasashen ketare

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Amnesty ta ce, hukumomi a Masar na tsare da daruruwan 'yan gudun hijiran Syria.

A sabon rahoton da ta fitar ta ce, a mafi yawancin lokuta ana tsare da yara ba tare da mahaifansu ba, kuma ana tsare da wasu 'yan gudun hijiran ne a ofisoshin 'yan sanda ba tare da basu abinci ko kula da lafiyarsu ba.

Haka kuma rahoton ya yi bayani game da wasu matasa biyu da aka mayar da su Lebanon, kasar da babu wani nasu, yayin da iyayensu ke Masar.

Masar dai bata maida martani game da rahoton na Amnesty ba, amma a baya ta sha zargin 'yan gudun hijiran Syria da goyon bayan kungiyar 'yan uwa Musulmi.