Sabbin hotunan bidiyo a kan harin da aka kai Kenya

Wasu masu sayyaya suna buya a firgice
Image caption Maharan sun razana masu sayayya a cikin natsuna

Wasu sabbin hotunan bidiyo na harin da aka kai cikin watan jiya a rukunin shaguna na Westgate dake birnin Nairobi sun nuna cikakkar razanar da masu sayayya suka yi da kuma halayya ta natsuwa ta wasu daga cikin maharan.

Hotunan, wadanda gidan Talabijin na Amurka CNN ya samu sun nuna irin rudamin da aka samu a lokacin da maharan suka fara bude ma masu sayayyar wuta.

Haka nan kuma sun nuna yadda maharan suka zamo cikin natsuwa, a wani lokaci ma suna magana ta wayoyin salula.

Hotunan bidiyon sun nuna cewar maharan sun samu lokacin ajiye bindigoginsu suka yi Sallah a lokacinda suka mamaye wurin.

Mutane akalla 67 ne dai aka kashe a lokacin harin.

Karin bayani