'Rufe ma'aikatun ya yi illa ga tattalin arzikinmu'

Image caption Obama ya ce babu wanda ya yi nasara sakamakon rufe ma'aikatun Amurka.

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya bayyana cewa kiki-kakar da aka yi kan kasafin kudin kasar da kuma rufe ma'aikatunta sun yi wa tattalin arzikin kasar illa ta babu-gaira-babu-dalili.

Mista Obama ya kara da cewa hakan ya rage kimar kasar a idon duniya, yana mai cewa babu wanda ya yi galaba sakamakon aukuwar lamarin.

Shugaban na Amurka ya bayyana haka ne sa'oi kadan bayan an sanya hannu kan wani kudirin doka da ya ba da damar sake bude ma'aikatun gwamnatin kasar.

Kasashen duniya dai sun yi maraba da sake bude ma'aikatun gwamnatin na Amurka.

Sai dai shugabar Asusun Ba da Lamuni na duniya, IMF, Christine Lagarde, ta yi kira ga Amurka ta rage yiwuwar fuskantar halin rashin tabbas wajen gudanar da harkokin kudi na gwamnati.

Karin bayani