An lalata kusan rabin makaman Syria

Masu binciken makamai masu guba a Syria
Image caption An sha takaddama tsakanin kasashen yamma, game da makamai masu guba na Syria

Hukumar yaki da bazuwar makamai masu guba a duniya ta ce, ta ci kusan rabin aikin lalata makaman da ta ke yi a Syria.

Sai dai hukumar ta nuna damuwa game da batun tsaro, wanda ta ce yana kawo mata tsaiko.

Wani kakakin hukumar ya shaida wa BBC cewa, dole ta sa masu binciken dake kan hanyarsu ta zuwa duba makamai a wani guri suka juya, saboda basu samu tabbaci tsaron lafiyarsu ba.

Ko da yake masu binciken sun nuna farin ciki a game da yadda aikin ke tafiya.