'Yan kasashen waje za su yi kati a Najeriya

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Sabon katin shaidar zama dan kasa da aka kaddamar a Najeriya, zai hada da 'yan kasashen waje da za su zauna a kasar na tsawon shekaru biyu.

Hukumar samar da katin shaidar zama dan kasa a Najeriya ta yi karin haske game da tsarin da shugaba Goodluck Jonathan ya kaddamar a ranar Alhamis.

Hukumar ta bayyana cewa ya zama wajibi ga kowanne dan kasa ya samu wata lamba da za a raba, kafin ya samu damar cin gajiyar abubuwa da dama nan gaba a kasar.

Haka kuma ta yi nuni da cewa bayanan da za a tattara zai taimaka ta fannin tsaro, musamman wajen kama masu laifi ko da bayan shekaru ne.

A baya dai an kashe makudan kudade wajen yin katin shaidar dan kasa a Najeriyar, amma aka yi watsi da shi.