Saudiyya ta juya wa kwamitin tsaro baya

Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Gwamnatin Saudiyya ta ce ba za ta karbi kujerar wucin gadin da aka zabe ba a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ba.

Kwana guda bayan zaben, hukumomin kasar sun ce sun dauki matakin ne saboda zargin cewar kwamitin tsaron na yin baki biyu wajen kawo zaman lafiya a duniya baki daya.

Saudi Arabia ta bayyana rashin jin dadinta a baya game da gazawar kasashen duniya wajen magance rikicin da ake yi a Syria inda 'yan adawa ke kokarin kawar da Shugaba Bashar al-Assad.

Rikicin Syria ta janyo mutuwar mutane fiye da dubu 100.

Karin bayani