Toyota zai janye motoci 885, 000

Motocin kamfanin Toyota
Image caption Kakakin kamfanin ya ce ba a samu rahoton wani mummunan hatsari ba a dalilin matsalar

Kamfanin kera motoci na Toyota zai janye motoci dubu 885, domin yin gyara ga matsalar da ka iya kaiwa a samu yoyon ruwa, a na'urar sanyaya motocin.

Kamfanin ya ce ruwan zai iya shiga cikin abin da ake kula da jakar dake kare matuki da fasinja, kuma za a iya samun tartsattsin wuta da zata kunna fitila domin gargadi.

Nau'oin motocin da Toyota zai janye sun hada da Camry da Camry Hybrid da Avalon Hybrid da kuma Venza, wadanda aka yi a shekarar 2012 zuwa 2013.

Za a janye motoci 847,000 daga arewacin Amurka, yayin da sauran kuma za a janye su daga nahiyoyin Turai da Asia da kuma Gabas ta tsakiya.