An zargi Nijar da karbar bashi a boye

Hama Amadou
Image caption Hama Amadou

Shugaban majalisar dokokin Nijar, Malam Hamma Amadou ya zargi gwamnatin kasar da karbo bashin dalar Amurka biliyan biyu ba tare da sanar da majalisar ba.

Malam Hamma Amadou, yace gwamnatin Nijar ta karbo bashin ne daga bankin Exim na kasar China bayan da ta jinginar da dukkan danyen man da Nijar din za ta fitar tsawon shekaru uku.

Shugaban majalisar dokokin ya baiyana haka ne yayin tafka muhawara game da tsige babban magajin garin Niamey da gwamnatin ta yi bisa zargin cin bashi ba bisa ka'ida ba.

Da yake mai da martani, ministan cikin gida Hasumi Mas'udu ya ce ba'a kammala yarjejeniyar neman bashin ba amma da zarar an gama gwamnati za ta gabatar da bayani ga majalisa domin neman amincewarta.

A watan Satumba ne dai gwamnatin ta tsige babban magajin garin Niamey Umarou Moumini Dogari daga mukaminsa bayanda ya jinginar da gidan gwamnati da ya ke ciki ya karbo bashin banki.