An bukaci Saudiyya ta sake shawara

Sarki Abdallah
Image caption Sarki Abdallah

Kasashen larabawa sun nemi Saudi Arabia ta amince ta karbi kujerarta ta kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, kwana guda bayanda kasar ta sanar da cewa ba ta bukatar kujerar ta wucin gadi.

Saudi Arabia dai ta zargi majalisar dinkin duniyar ne da nuna bambanci tare da bayyana takaicinta game da gazawar majalisar wurin daukar mataki game da rikicin Syria.

Sai dai a wata sanarwa da su ka fitar, wasu jakadun kasashen larabawa sun bukaci Saudi Arabia ta karbi kujerar domin kare batutuwan da su ka shafa larabawa da kuma addinin Musulunci a majalisar dinkin duniya.