Sojojin Syria goma sha shida sun mutu

Harin Jarmana
Image caption Harin Jarmana

Masu fafutuka a Syria sun ce akalla dakarun Syria goma sha shida sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wani bam a mota da kuma gwabzawa da masu tada kayar baya a wajen garin Damascus babban birnin kasar.

Kafar yada labaran Syria ce ta rawaito labarin harin bam din a yankin inda ta ce akwai wadanda suka samu raunuka da dama sakamakon harin.

Kafar yada labaran Syria ta bayyana harin a matsayin ta'adanci.

Amma daga bisani rahotanni daga masu fafutuka sun nuna cewa, harin kunar bakin wake ne na mota da aka kaddamar a wani bangare na farmakin 'yan tawaye akan Jarmana daga kewayen garin Mliha wanda ke karkashin 'yan Tawaye

An ruwaito Dan kunar bakin waken wanda ya fito daga kungiyar Nusra wacce ke da alaka ya danawa kansa bom a wani wajen duba ababan hawa na sojoji kusa da wata masana'anta wacce a lokacin da ta kasance wani wurin da ake fafatawa inda bangaren gwamnati ke kai hare-hare ta sama da kuma amfani da makaman atilari domin fatattakar 'yan tawayen su koma baya

Amfani da hare-haren kunar bakin wake wani salo ne da 'yan Tawaye su ke kara yawaita kara amfani da shi a hare-haren da su ke kaddamarwa, bangaren gwamnati kuwa an ruwaito cewa na amfani da hari ta sama a artabun da ake yi a Dir az Zor.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba