Amurka ta nemi Syria ta bari a kai agaji

Yarinya a Syria
Image caption Yunwa ta addabi Syria

Amurka ta bukaci Syria ta kyale a kai kayan agaji ga yankunan kewayen birnin Damascus da ke hannun 'yan tawaye, wadanda sojinta su ka yi wa kawanya tsawon watanni.

Amurkan tace fararen hula a yankunan na tsananin bukatar abinci, da ruwa da kuma magunguna.

Ta bada hujja da rahotannin da ke cewa kananan yara na rasuwa saboda rashin wadatar abinci a wuraren da ke da nisan kilomitoci kadan daga fadar shugaba Assad.

Hotunan da BBC ta samu daga unguwar Yarmouk sun nuna yadda iyali ke shan wuya wurin neman abinci.

Rundunar sojin Syria dai ta ce wajibi ne yankunan da ke hannun 'yan tawayen su mika wuya ko kuma yunwa ta hallaka su.