An kai hari wani Coci a Masar

Hambararren shugaban Masar Muhammad Morsi.
Image caption Kasar Masar ta ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Muhammad Morsi a watan Yulin da ya gabata.

Mutane uku ne suka rasa rayukansu ciki har da yarinya 'yar shekaru 8, a lokacin da wasu 'yan bindiga suka bude wuta a wajen wani Cocin kiristoci Kibdawa da ake shagalin biki a birnin Alkahira.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi harbin kan mai uwa da wabi ne a lokacin da kiristoci ke barin Cocin da ke garin Giza.

Ministan cikin gida ya ce akalla mutane tara ne suka jikkata.

Kiristoci Kibdawa a kasar Masar na fuskantar barazanar hari daga masu tsattsauran ra'ayin addinin musulunci, inda ake zargin su da marawa sojojin kasar baya wajen hambarar da gwamnatin Muhammad Morsi a watan Yulin wannan shekarar.

Karin bayani