Fargabar karuwar gobarar daji a Australia

Gobarar daji a kasar Australia
Image caption Gobarar daji a kasar Australia

'Yan kwana-kwana a jihar New South Wales ta kasar Australia na fargabar karuwar gobarar daji.

Hasashen yananyi na nuna cewa za'a samu karin zafin rana da iska mai karfi, abinda zai kara rura wutar dajin da ake fama da ita a yankin.

Gobarar dajin ta bana dai ita ce mafi muni a cikin shekaru goma, inda tuni ta kone fiye da gidaje dari biyu.

Magajin Garin Blue Mountains Mark Greenhill ya yi gargadin cewa akwai sauran gobarar dajin a gaba.