An kashe mutane 6 a garin Gamboru

Borno Najeriya
Image caption Sojojin Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun kashe a kalla mutane shida a kan hanyar garin Gaboru da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Mazauna garin Gamborun sun bayyana cewa tun gari bai gama wartsakewa ba maharan suka bakunci yankin, kuma suka datse hanyar da ta tashi daga garin zuwa Maiduguri.

Sun ce maharan sun kashe matafiya tare da jikkata wasu.

Sun kuma ce kusan wannan ne karon farko da aka kai hari gab da garin nasu, don haka hankalinsu ya yi matukar tashi.

BBC ta yi kokarin tuntubar kakakin Rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Borno, dangane da wannan harin, amma hakan ba ta samu ba.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Jihar Borno da wasu jihohi a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya dai na fama da hare-hare da ke haddasa asarar rayukan jama'a da dama.

Yayin da kungiyar jama'atu ahlissunnah lidda'awati wal jihad da aka fi sani da boko-haram ke ikirarin kai wasu daga cikin hare-haren, wasu kuma ana dangantawa da 'yan fashi.

Yawaitar hare-haren ce ma ta sa gwamnatin tarayyar kasar sanya dokar ta-baci wa jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.