Tarihin Maryam Ahmed Sabo

Image caption Barrister Maryam Ahmed Sabo

_Maryam Ahmed Sabo ita ce babbar mai shari'a kuma mataimakiyar rajistara a ma'aikatar shari'a ta jihar Kano, da kuma Babbar kotun jihar.

Ana yanke hukunci a kan shari'ar da ta danganci manyan laifuka da laifukan da suka shafi zamantekewa.

Mace ce da ta kware a harkokin shari'a, inda ta kwashe fiye shekaru 18 tana wannan fanni.

Ita ce mai shari'ar da ke kula da shari'ar da ta shafi laufukan da yara ke aikatawa.

Kazalika, Maryam Sabo tana fafutikar kare hakkin dan adam --- ta fi ba da muhimmanci wajen kare hakkin mata da kananan yara da bayar da shawarwari da kuma wayar da kan mata game da fyade da cin zarafin mata a jihar Kano.

Maryam Sabo ta yi karatunta na dipiloma a kan shari'ar addinin musulinci da dokokin zamantakewa, kana ta yi digiri a wannan fanni dukka a Jami'ar Bayero da ke Kano a shekarar 1991.

Ta zama cikakkiyar lauya a shekarar 1993.

Haka kuma Maryam Sabo ita ce shugabar hadaddiyar kungiyar lauyoyi mata ta Nigeria reshen jihar Kano.