Boko Haram: Direbobi na cikin fargaba

Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Direbobi da matafiya a jihar Borno dake arewacin Najeriya, sun ce suna cikin fargaba, saboda yawan hare-haren da 'yan bindigar da ake zargin 'yan Boko Haram ne ke kai masu.

Ko a ranar Lahadi ma sai da wasu 'yan bindigar suka datse hanyar Gamboru Ngala zuwa Maiduguri, inda suka hallaka matafiya dayawa.

Bayanai sun ce harin baya bayanan da wasu 'yan bindiga dake sanye da kayan soji suka kaiwa matafiya a garin Gamboru ya yi sandiyyar mutuwar mutane da dama.

Duk da irin wannan barazanar, matafiya sun ce za su ci gaba da bin hanyoyin jihar Borno kamar yadda wani direba mai bin hanyar Gamboru ya shaidawa BBC ta wayar tarho

Yace "Abin ya kai, inna naha. Sun bude mana wuta muna kan hanya, abinda yasa muka ranta ana kare zuwa daji".

Ya kara da cewar " duk da irin matsalar, zamu ci gaba da bin hanyoyin jihar Borno".

Karin bayani