Westgate:Sojojin Kenya sun debi ganima

Image caption Sojoji dauke da fararen lodoji cike da kayayyakin jama'a

Wani sabon hoton bidiyon da aka samu game da harin da aka kai a cibiyar kasuwanci ta Westgate dake Nairobi a kasar Kenya, ya nuna yadda sojoji ke dibar kayayyakin jama'a.

Sabon bidiyon da kafofin yada labaran Kenya suka samu, wanda kuma an nade shi ne da kyamarar tsaro ta CCTV, ya nuno sojan Kenya suna fita daga wani babban shago mai suna Nakumatt kowannensu dauke da abinda ya wawura a cikin babbar leda irinta cefane.

A cikin bidiyon an nuno sojoji suna bude wasu fararen kwalaye daga a cikin wani shagon da bisa ga dukkan alamu na saida wayar salula ne.

A lokacin harin da 'yan al-Shabab suka kai a ranar 21 ga watan Satumba a Westgate din, mutane akalla 67 ne suka rasu.

Karin bayani