Alhazan Najeriya sun koka game da abinci

Wasu Mahajjatan Najeriya
Image caption Wasu Mahajjatan Najeriya

Yayin da ake kokarin maido da mahajjatan Najeriya gida daga kasar Saudiyya bayan kammala aikin Hajjin bana, wani batu da mahajjatan na bana daga kasar suka koka akai shine na rashin ingancin abincin da hukumomin aikin hajjin kasar ta ba su a lokacin zaman da suka yi a muna da kuma tsayuwar Arfat.

Mahajjatan dai sun ce sun biya makudan kudade kari kan kudin aikin hajjin a zaman na abinci ga hukumomin amma wanda aka basu ba ya da ingancin da ya kama ce su.

Aikin na Hajji dai yana bukatar kuzari sosai saboda wahalar da ke cikinsa saboda haka samun abinci mai kyau yana da matukar muhimmanci ga mahajjatan.

Rahotanni sun ce a karshen makon daya gabata ne aka fara jigilar dawo da alhazan Najeriya zuwa gida bayan da suka kammala aikin Hajji.