'Yan PDP sun gwabza a Kano

Dr Rabi'u Musa Kwankwaso
Image caption Gwamnan jihar Kano, Dr Rabi'u Musa Kwankwaso

A Najeriya, bangaren shugabancin jam'iyyar PDP a jihar Kano dake goyon bayan shugabancin Bamanga Tukur sun zargi bangaren magoya bayan gwamnan jihar da afka musu a lokacin da suke gudanar da taro, abin da ya janyo jikkatar mutane da dama.

'Yan bangaren PDP din da ke goyon bayan shugabancin Bamanga Tukur din dai sun yi zargi cewa 'yan Kwankwasiyya ne suka kai musu farmaki a sabon ofishin jam'iyyar.

Sai dai bangaren gwamnan jihar Kano Dr Rabi'u Musa Kwankwaso sun musanta zargin cewa magoya bayan su ne suka kai harin.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane hudu da take zargin su da hannu a wannan al'amari.