An kashe mutane kusan 70 a Sudan ta Kudu

Wani mayaki a Sudan ta Kudu
Image caption Wani mayaki a Sudan ta Kudu

Rahotanni daga Sudan ta kudu na cewa, yawan mutanen da aka kashe ya zuwa yanzu yayin tashin hankalin da aka yi a jihar Jonglei ranar Lahadin da ta gabata ya kai mutane saba'in da takwas.

Dan majalisar dokoki a yankin da lamarin ya auku, Deng Dau ya fadawa BBC cewa, an yi amfani da jirgin sama mai saukar ungulu wajen kwashe mutane da dama da suka jikkata.

Ministan yada labaran kasar, Micheal Makuie, ya kare zargin gazawar gwamnatin wajen samar da tsaro, yana mai cewa gwamnati na iya kokarinta, ta hanyar amfani da dan abinda take da shi wajen samar da tsaro ga jama'ar kasar.

Wasu da suke tsira daga harin sun ce, 'yan kabilar Murlay ne suka kai harin.