Za'a yi taro a london kan rikicin kasar Syria

 Kasar Syria
Image caption Wuraren da aka lalata a Kasar Syria

Nan gaba a yau ne shugabannin kasashen yamma da na larabawa za su gana da shugabanin 'yan tawayen Syria a birnin London, don kokarin shawo kan su shiga tattaunawar sulhun da za a yi a wata mai zuwa a Geneva.

Manyan jagororin 'yan adawa da suka hada da hadakar gamayyar 'yan adawa ta Syrian National Coalation sun ce ba su da niyyar tattaunawa da wakilan shugaba Assad.

Jami'ai daga kasashen yammacin turai dai sun ce samu kwarin guiwar shirya wannan taro ne ganin irin sakamakon da aka samu dangane da shirin lalata makamai masu guba na kasar Syriar.

Sai dai a wata hira da ya yi da wani gidan talbijin na kasar Lebanon mai suna al-Mayadeen, shugaba Bashar al-Assad ya jaddada cewa tilas 'yan kasar sa su kasance cikin duk wata tattaunawa ta neman warware rikicin kasar da aka shafe watanni 31 ana yi.