Boko Haram: Cocin Anglican ya damu

Image caption Rabaran Nicholas Okoh

A daidai lokacin da ake ci gaba da hallaka wasu matafiya a yankin arewa maso gabashin Najeriya, duk kuwa da dokar ta-bacin da aka kafa, cocin Anglican a Najeriyar ya yi kira ga gwamnati da ta kara daukar tsauraran matakai a kan 'yan kungiyar Boko Haram, wadanda ake zargi da yin aika-aikar.

Shugaban cocin ne, Rabaran Nicholas Okoh, ya bayyana hakan jim kadan bayan taron mako guda da cocin Anglican yayi a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Yace: "A matsayinmu na coci, abu na farko da zamu fara nema shi ne gwamnati ta samar mana da tsaro, domin mu samu sukunin yin ibada cikin kwanciyar hankali".

Rabaran Okoh ya kara da cewar " duk kokarinmu na tattaunawa da malaman addinin Musulunci, bai haifar da wani sakamako ba, domin su 'yan Boko Haram din sun ki sauraron kowa, suna cewa za su ci gaba da gwagwarmaya, sai sun ga sun hana ilmin Boko , ko sun shimfida shari'ar Musulunci a duk fadin kasa".

Karin bayani