Assad baida rawar da zai taka a Syria

Image caption William Hague da John Kerry

Birtaniya ta ce shugabannin kasashen yammacin duniya da na Larabawa sun amince a kan cewar Shugaba Bashar al-Assad baida rawar da zai taka a gwamnatin da za a kafa nan gaba a Syria.

Sakataren harkokin wajen Birtaniyar ne, William Hague ya bayyana hakan, a lokacin taron da suke yi a London

Birtaniya kuma ta ce, yana da mahimmanci matuka 'yan adawar Syria masu sassaucin ra'ayi su shiga tattaunawar da za a yi a kan makomar kasar da za a yi a Geneva a watan gobe.

'Yan adawan Syria da dama sun ce ba za su shoga ciki tattaunawar ba, idan har Shugaba Assad na kan mulki.

A tattaunawarsa da wani gidan talabijin, Shugaban Assad ya kara saka ayar tambaya game da hallacin 'yan adawar Syria, inda yace basa wakiltar al'ummar kasar.

Karin bayani