An samu raguwar mutuwar yara a Nijar

Kananan yara dake kwance a asibiti a Niger
Image caption Kananan yara dake kwance a asibiti a Niger

Wani sabon rahoto da kungiyar bada agaji ta Save the Children ta fitar, ya ce Jamhuriyar Nijar ce kasar da ke sahun gaba a duniya wajen kokarin rage mutuwar kananan yara.

Rage mace-macen kananan yaran dai na daga cikin muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya, da ake son cimma nan da shekarar 2015.

Kungiyar ta ce shekarar 1960, kashi 27 cikin dari na kananan yara ne ke mutuwa a nahiyar Afrika, sai dai a yanzu adadin bai kai kashi goma ba cikin dari.

Sai dai ba dukkan kasashe masu tasowa ba ne suka yi kokarin rage wannan matsalar ta mace-macen kananan yara kamar yadda ake bukata.