Za'a yi rigakafin cutar sankarau a Kaduna

Gwamna Muktar Ramalan Yero
Image caption Gwamnan jihar Kaduna Muktar Ramalan Yero

Hukumomin lafiya a jahar Kaduna ta Najeriya na shirin kaddamar da wani shirin rigakafin cutar sankarau da zai hada har da manya da shekarun su ba su kai talatin ba.

Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta jahar ta ce ta na sa ran yiwa mutane miliyan biyar rigakafin a karkashin wannan shirin, wato sama da kashi saba'in cikin dari na al'ummar jahar.

Wannan dai ya biyo bayan yanayin zafi mai tsanani da ya fara kunno kai a jahar.

Sai dai wasu 'yan jihar na nuna shakku dangane da iya cimma wannan burin a wannan shirin rigakafin da za'a fara a makon gobe.