Malaman Saudiyya na adawa da tukin mata

Image caption Malamai na matukar adawa da tukin mata

Malamai fiye da 100 ne a Saudi Arabia suka nufi kotun da ke Riyadh domin yin adawa da matsin lambar da wasu ke yi wajen ganin an janye hanin da aka yi wa mata na tuki.

A wani bidiyo da aka sanya a shafin Youtube, wani malami ya ce sun je kotun ne domin su shaidawa Sarki Abdullah cewa akwai babban hatsarin da kasar ke fuskanta.

Sarkin dai da ma manyan jami'an gwamnatinsa ba sa nan lokacin da malaman suka je kotun.

Mutane fiye da 16, 000 ne suka sanya hannu kan wata takarda domn goyon bayan kamfe din da ake yi na kalubalantar hana mata yin tuki.

Ranar Asabar mai zuwa ne ake sa rana wasu mata za su nuna bukatarsu ga hukomi domin a bar su su ria yin tuki.king