'Yan Birtaniya 50 na da alaka da Al-Shabaab

Image caption Mayakan Al-shabab a Somalia

BBC ta tabbatar cewa akwai sunayen mutane kusan 50 'yan Birtaniya da ke da alaka da kungiyar Al-Shabaab ko kuma wasu kungiyoyin irinta.

Galibinsu sun je Somalia domin yaki tare da kungiyar ko kuma suna kokarin yin hakan.

Al Shabaab, wacce ke Somalia, ta dauki alhakin harin da mutane da dama suka mutu a cibiyar kasuwanci ta Westgate da ke kasar Kenya.

Lauyoyin iyalan daya daga cikin 'yan Birtaniya kuma dan kungiyar Al-Shabaab wanda ya mutu a Somalia, sun soma bincike a kan cewa ko an kashe shi ne a wani samamen da dakarun yammacin duniya suka kai.

'Rashin tabbas'

Sunayen mutane 47 da BBC ta tattara, ta yi amfani ne da majiyoyi da dama ciki har da bayanai daga kotuna a Birtaniya da kuma kasashen waje da wasu bayanai na musamman.

Image caption Mayakan Al-Shabab

Wannan jerin shi ne cikakken sunayen 'yan Birtaniya da ake zargin suna gwagwarmaya tare da kungiyar.

Binciken ya nuna cewar jami'an tsaro sun tabbatar da sunayen mutane 32 wadanda suka je suka yi fada tare da kungiyar Al-Shabaab.

Akwai kuma sunayen mutane bakwai da ke gaban kotun a Birtaniya wadanda suka yi kokarin shiga Somalia, amma aka gano su aka kuma wargaza shirin.

Sauran kuma ana zarginsu ko kuma an kama su da laifin tara kudi don kungiyar al-Shabaab, ko kuma kokarin taimaka wa wasu su je kasar.

Bakwai daga cikinsu tabbas son koma Birtaniya, kuma kawo yanzu ba a san makomar galibin sauran ba.

Hudu daga cikin mazan da ke jerin sun mutu, har da wasunsu da aka gani a wani bidiyo da al-Shabab ta fitar a kwanan nan.

Karin bayani