"Kasar Chadi na keta hakkokin bil'adama"

Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi
Image caption Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi

Kungiyar kare hakkokin Bil Adam ta Amnesty International ta koka game da keta hakkokin bil'adama da gwamnatin shugaba Idriss Deby na kasar Chadi ke yi.

A wani sabon rahoto data fitar, kungiyar ta ce mutane da dama ne aka tsare su da bisa zargin cewa suna shirya wa gwamnatin kasar makarkashiya, sannan kuma ba'a gurfanar da su a gaban kotu.

Yanzu haka dai daruruwan jama'a ne da suka hada da 'yan majalisar dokoki bangaren adawa da 'yan jarida tare da malaman jami'o'i ake tsare da su ba bisa ka'ida ba a kasar.

Amnesty ta bukaci hukumomin kasar Chadi da su ta shi tsaye wajen ganin sun sauya irin yanayin da ake ciki a kasar musamman batun kare hakkokin bil'adama.