Facebook ya sauya matsayi kan bidiyo

Dandalin sada zumunta na facebook
Image caption Masu baiwa kamfanin shwara na ganin bidyo ma tayar da hankali zai iya tasiri mara kyau a rayuwar matasa

Dandalin sada zumunta na Facebook ya cire wani hoton bidiyo dake nuna yadda aka cire wa wata mata kai, sannan ya sanya wasu sabbin dokoki kan irin abubuwan da za a iya sawa a shafin.

Hakan sauya matsayi ne a matakan da Facebook ya dauka kwanaki biyu da suka gabata, na janye haramcin da ya yi game da sanya hotunan bidiyo na tashin hankali.

Matakin da ya gamu da sukar Firai ministan Birtaniya da kuma masu baiwa kamfanin shawara game da kariya.

Ko da yake Facebook ya jaddada cewa har yanzu zai bar mutane su sanya hotuna ko zane-zane, amma zai yi nazari sosai game da abin da suka kunsa.