Jamus da Amurka na cacar baki

Image caption Merkel ta shaidawa Obama wannan cin amana ne

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta gayyaci jakadan Amurka a kasar don ya amsa tambayoyi bisa zargin cewar jami'an leken asiri sun yi satar nadar wayar tarhon Shugabar Jamus, Angela Merkel.

Ambasada John Emerson nan gaba a yau zai gana da Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle kan wannan babban zargin.

A ranar Laraba, Ms Merkel ta tattauna da Shugaba Obama a kan wannan zargin, inda tace masa wannan cin amana ne.

Amurka ta karyata satar sauraron wayar Ms Merkel, kuma ta ce bata taba yin haka ba.

Kwamishinan kula da kasuwannin cikin gida na tarayyar Turai, Michel Barnier ya ce Turai za ta gina wani tsari na musamman game da na'urar intanet wanda baya karkashin kulawar Amurka.

Karin bayani