China da India sun kulla yarjejeniya

Image caption Piraministan India, Manmohan_singh da Li Keqiang na China

China da India sun sanya hannu a yarjejeniyar hadaka don kare tsaron kan iyakokin kasashen biyu, bayan da a farkon wannan shekarar suka samu rashin jituwa.

Yarjejeniyar ta soji za ta habbaka yadda ake samun bayanai tsakanin kasashen biyu.

A jawabinsa a Beijing bayan tattaunawarsa da takwarassa na India, Manmohan Singh, Piraministan China, Li Keqiang ya ce za su tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakaninsu.

Kasashen biyu na takaddama ne kan batun iyakar kasashen ta Himalayan abinda a shekarar 1962 ya jefa su cikin dan karamin yaki.

Karin bayani