Jamus ta yi wa Amurka kashedi

Shugabannin Jamus da Amurka
Image caption Shugabannin Jamus da Amurka

Hukumomin kasar Jamus sun ce, suna kyautata zaton hukumar leken asirin Amurka tana satar dukkan bayanai dake shiga da kuma fita daga wayar salula shugabar gwamnatin kasar, Angela Merkel.

Kakakin gwamnatin Jamus Steffen Seibert yace, shugabar gwamnatin Jamus din tayi magana da shugaba Obama akan wannan batu inda ta nemi karin bayani daga bangaren Amurka.

Jay Carney shi ne kakakin fadar White House, ya kuma ce shugaba Obama ya bata tabbacin cewa, Amurka bata taba satar bayanai daga wayar salular shugabar gwamnatin Jamus ba, kuma shugaba Obama ya bata tabbacin cewa, Amurkan ba zata taba aikata hakan ba.