Shugaba Jonathan na ziyara a Israila

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya soma ziyarar ibada a kasar Israila.

Wannan shi ne karon farko da wani shugaban Najeriya da ke kan mulki zai kai ziyara Israila don gudanar da ibada.

Kakakin fadar shugaban kasar ya ce shugaba Jonathan zai gana da shugaba Shimon Perez da kuma frai minista Benyamin Netanyahu.

Haka kuma ana sa ran shugaba Jonathan zai gana da 'yan Majalisar dokokin kasar da kuma shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas.