An kama saurayi da ake zarginsa da fyade

Image caption 'Yan sanda na farautar samarin da ake zargi da fyade

Rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa a Najeriya ta kama daya daga cikin wasu samari uku, wadanda ake zargin sun taru sun yi wa wata yarinya fyade.

Mai magan da yawun Rundunar a Jihar Bayelsar, ya ce ragowar samarin biyu sun arce amma suna neman su don su fuskanci sharia.

Daga bisani an yi zargin yarinyar da aka yi wa fyaden ta kashe kanta; don takaicin aika-aikar da ake zargin samarin sun yi mata.

Batun fyade dai yana daya daga cikin miyagun laifuffukan da ke ci gaba da zama wata gagarumar matsala a Najeriya.

Karin bayani