'Yan fashin teku sun sace Amurkawa a Nigeria

Image caption An sace direba da injiniyan jirgin

Wasu 'yan fashin teku sun kai hari kan wani jirgin ruwan Amurka da ke dauke da mai a gabar tekun Nigeria, sannan suka sace matukin jirgin da injiniyansa.

Jirgin ruwan, mai suna The C-Retriever, mallakin kamfanin sufurin jiragen ruwa Amurka ne da ake kira Edison Chouest Offshore.

Rahotanni sun ce an kai wa jirgin ruwan hari ne ranar Laraba, amma sai ranar Alhamis labarin ya fito.

Hare-haren 'yan fashin teku na ci gaba da karuwa a gabar tekun Guinea.

An kashe akalla sojojin Nigeria guda biyu ranar Talata lokacin da 'yan fashi suka kai wa wani karamin jirgin ruwa wanda ke dauke da ma'aikatan gine-gine a yankin Niger Delta.

Karin bayani