Kotu ta yi watsi da daukaka karar BO Xlai

Image caption Bo_Xlai bai samu nasarar daukaka kara ba

Wata Kotu a kasar China ta yi watsi da daukaka karar da dan siyasar nan da ya bai wa kasar sa Kunya watau Bo_Xlai; dangane da tuhumar da aka yi masa game da cin hanci da rashawa.

Wannan na nufin, Bo_Xlai din zai yi zaman gidan Yari na daurin rai-da-rai, hukuncin da tun farko aka yanke masa.

Mr Bo, a wani lokaci yana cikin gaggan 'yan siyasar kasar da tauraruwarsa ke haskawa, har ma ana tsegunta cewa zai zama jagoran jam'iyyarsa, amma lokaci guda martabarsa ta dakushe bayan an zargi Matarsa da laifin kisan wani dan kasuwa dan Birtaniya.

Wannan dai wata tabargazar siyasa ce mai girma da aka dade ba a yi irin ta ba a kasar ta China.

Karin bayani