Mata na kokarin kan-kan-kan da Maza

Image caption Gibi tsakanin Mata da Maza na raguwa a Duniya

Wani sabon rahoto ya nuna cewar a 'yan shekarun nan rayuwar Mata da Maza a sassa daban-daban na duniya ta yi kan-kan-kan da ta Maza.

Rahoton binciken na shekara-shekara da hukumar nazarin harkokin tattalin arziki na kasashen duniya ta gudanar ya nuna cewar tattalin arzikin Mata ya daidaita da na Maza, kuma Matan sun kara samun cigaba ta fuskar shiga harkokin mulki ko siyasa.

Sai dai kuma cigaban da suka samu ba shi da yawa, a wasu kasashe hamsin ma babu wani cigaban da suka samu.

kasashen da Matan ke koma-baya sun hada da Chadi da Pakistan da Yemen.

Karin bayani