An kubutar da 'yan gudun hijira 700 a Sicily

Image caption Hukumomin Italiya sun ce galibin mutanen da Syria suke

Hukumomin Italiya sun ce sun kubutar da 'yan gudun hijira sama da dari bakwai a wasu samame da suka kai na tsawon dare, a mashigin ruwa na Sicily.

Da dama daga cikin mutanen sun tsere ne daga Syria.

Aikin samamen na daga wani bangare na matakan da Tarayyar Turai ta fara dauka na tsaurara sintiri, bayan mutuwar wasu bakin haure su sama da dari uku bayan da jirgin ruwanda suke ciki ya kife a tekun Italiyar a farkon watan nan.

Irin wannan aikin kubutarwa kusan ya zama ruwan dare, kuma ana kai galibinsu tsibirin Lampedusa.

Karin bayani