'Soji sun kashe 'yan Boko Haram 74 a Borno'

Image caption Sojin sun ce sun kai samame ne sansanin 'yan Boko Haram

Sojojin Nijeria sun ce kashe wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram 74 a samamen da suka kai jihar Borno.

Wata sanarwa da ta fito daga rundunar sojojin ta ambato Laftanar Kanar Mohammed Dole yana cewar an kai harin ne ta kasa da ta sama ranar Alhamis a sansanonin 'yan kungiyar da ke kauyukan Galangi da Lawanti na Jihar Borno.

Laftanar Kanar Dole ya kara da cewa wasu daga cikin 'yan kungiyar sun tsere da raunika a jikinsu.

Ya ce sojoji ne suka kai harin tare da goyon bayan mayakan sama wadanda kuma suka rusa sasanonin da ake zargin na 'yan kungiyar ta Boko Haram na fakewa.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labari.

Karin bayani