Jami'an Afrika sun soki Ban Ki Moon

Image caption Ban Ki Moon

Jami'an diplomasiyyar Afrika sun ce ba su ji dadin cewa sakatare janar na Majalisar Duniya Duniya, Ban Ki Moon ya bada shawarar tura karin sojoji kimanin 4,500 ne kawai, domin tunkarar mayakan al Shabaab a Somalia.

Ita dai Tarayyar Afrika ta bukaci a bata karin sojoji sama da 6,000.

A halin yanzu ana da sojoji 8,000 na kasashen duniya a Somalia.

A wani rahoto ga kwamitin sulhu na Majalisar Duniya Duniya, Mr Ban ya ce idan ba an tura karin sojojin ba, akwai hadarin cewa hannun agogo ya koma baya dangane da nasarorin da ake samu a kan 'yan kungiyar al-Shabaab.

Karin bayani