Kenya na kokarin dakile harin ta'addanci

Image caption Kenya za ta fara mayar da 'yan gudun hijira daga Somalia

Gwamnatin Kasar kenya na lalubo hanyoyin da za ta kaucewa harin ta'addanci a kasar bayan mummunan harin da aka kai West-gate.

Harin dai wanda Kungiyar Al-shabaab ta dauki alhakkin kai wa ya jawo asarar rayuka da dama.

Ministan harkokin cikin gidan Kenya ya ce, gwamnatin kasar za ta mayar da 'yan gudun hijira daga kasar somalia zuwa kasar su a wani mataki na kaucewa sake fuskantar harin ta'addanci a kasar.

Ministan, Joseph Ole Lenku ya ce, ya zuwa yanzu gwamnatin kasar ta kori jami'an hukumar shige da fice su goma sha biyar dake aiki a kasar, a cigaba da binciken da take yi dangane da harin nan na Westgate.

Karin bayani