Mummunan harin bam a Mosul na Iraqi

Ta'asar harin bam a Bagadaza
Image caption Ta'asar harin bam a Bagadaza

A Iraki akalla mutanen hamsin ne suka hallaka, kuma dayawa suka raunata, sakamakon hare-haren bam da aka kai da motoci.

Yawancin mutanen sun mutu ne a hare-haren da aka tsara kaiwa a birnin Bagadaza,a unguwanni inda 'yan Shi'a ke da rinjaye:

Wannan mutumin ya ce, an kona motoci, kuma an lalata shaguna.

Harin da ya fi muni shine wanda aka kai a birnin Mosul na arewacin Irakin.

A nan wata mota ce ta tarwatse a gaban wani banki, inda sojoji suka ja layi don karbar albashinsu.

Akalla mutane goma sha biyu ne suka rasu a wurin, cikinsu har da fararen hula.

A shekaru biyar din da suka wuce ba a taba samun tashin hankalin da yayi muni irin haka ba a Irakin.

A wannan watan kawai, in ji wakilin BBC a Bagadaza, kimanin mutane dari hudu aka hallaka.

Karin bayani