'Gwamnonin sabuwar PDP za su fice daga jam'iyyar'

Image caption Gwamnonin sabuwar PDP a ziyararsu zuwa majalisar wakilan Najeriya

'Yan bangaren sabuwar PDP a Najeriya sun ce sun fara nazarin kafa sabuwar jam'iyya ko sauya-sheka zuwa wata.

Sai dai bangaren ya ce ba zai janye daga tattaunawar da yake yi da shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan ba, har sai abu ya gagara.

Wannan bangare dai ya kwashe watanni yana takun-saka jam'iyyar karkashin jagorancin Alhaji Bamanga Tukur, yana zargin cewa jam'iyyar ta saba wa akidar da aka kafa ta a kanta, har ya bukaci a sauke shugaban daga mukaminsa.

Mr Eze Chukwuemeka shi ne sakataren yada labaran bangaren sabuwar PDP "mun tattauna a kan zabin da muke da shi na fara tuntubar wasu jam'iyyun siyasa da nufin sauya sheka da kuma duba yiwuwar kafa sabuwar jam'iyyar siyasa"

Ya kara da cewar "Jam'iyyun siyasa da dama na zawarcinmu, saboda sun san cewa duk wadda muka hada kai da ita to ita ce za ta lashe zabe a shekara ta 2015".

Karin bayani