Mutane 65 sun mutu a harin bam a Iraqi

Image caption Mutane da dama sun hallaka sakamakon bam a Iraqi

A Iraqi, a kalla mutane sittin da biyar ne suka hallaka, wasu masu yawa kuma suka jikkata, sakamakon hare-haren bam da aka kai da motoci.

Yawancin mutanen sun mutu ne a hare-haren da aka kai birnin Bagadaza, a unguwanni na galibi 'yan Shi'a.

Wata kasuwa dake cike da mutane da wata tashar mota na daga cikin wuraren da aka kai harin.

Hari guda daya mafi muni shine wanda aka kai a Birnin Mosul dake arewacin kasar lokacin da wata mota ta tarwatse a gaban wani banki wurin da sojoji suka yi layi don karbar albashinsu.

Tun shekaru biyar da suka wuce, ba a taba samun tashin hankalin da ya yi muni irin haka ba a kasar ta Iraqi.

Karin bayani