Kishin ruwa ya kashe 'yan Nijar a hamada

Image caption Shugaban Nijar, Alhaji Muhammadou Issoufou

'Yan Nijar su talatin da biyar sun mutu sakamakon kishin ruwa a cikin hamada bayan da motar da suke ciki ta kakare a kan hanyarsu ta zuwa Algeria.

Magajin garin birnin Agadez, Rhissa Feltou ya shaidawa BBC cewar mutane sittin ne wadanda suka hada da mata da kananan yara wannan abun ya shafa, amma mutane kamar 35 ne suka rasa rayukansu.

Jami'an tsaro sun dauke mutane 19 da suka tsira da ransu zuwa garin Arlit.

A cewar magajin garin motoci biyu ne ke dauke da 'yan ci ranin zuwa kasar Algeria kafin daya ta lalace.

'Yan Afrika da dama suna balaguro zuwa kasashen waje domin neman ingantaccen rayuwa saboda talaucin daya addabesu a kasashensu.

Karin bayani